Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen mako ya yi tir da harin da aka kai wa ‘yan banga a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda aka yi asarar rayuka da dama.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina a ranar Juma’a ta tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar ‘yan banga ‘Yansakai su 41 a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai a dajin Yargoje.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uba Ya Fashe Da Kuka Bayan Ya Ga Ƴar sa Da Jarirai Biyu
‘Yan ta’addan sun yi wa ayarin ‘yan banga kwanton bauna a cikin dajin a lokacin da suke kokarin kwato shanun da suka sace wanda ya kai ga kisan.
Da yake mayar da martani, Buhari ya jinjinawa dukkan ‘yan banga da ‘yan uwa da suka yi shahada, inda ya ce ba za a manta da sadaukarwar da jajirtattun maza da ke aiki don dakatar da hukunta miyagun laifuka a cikin al’ummarsu ba.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a ranar Lahadi.
“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da iyalan wadanda suka mutu a cikin wannan mawuyacin lokaci. Allah ya jikan mamaran,” in ji Shugaban.
A wani labarin kuma,Da Ɗuminsa: Gwamnan Jigawa ya amince da naɗa sabon Sarkin Dutse
Gwamnan Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse
Gwamnan JIhar Jigawa Badaru Abubakar ya amice da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse, domin maye gurbin mahaifinsa wanda ya rasu a makon jiya.