Wani bidiyo wanda yadu a kafafen sada zumuntar zamani ya nuna yadda mahaifin wata amarya ya kwashi rawar burgewa yayin shagalin auren, Inside Arewa News ta wallafa.
Ga dukkan alamu fili guda aka buda masa wanda duk taron mata ne, amma sai aka ba shi fili tare da diyarsa inda suka kwashi rawa son ran su.
KU KARANTA: Rayuwa kenan: Amarya ta kwanta dama kwanaki kaɗan bayan aurenta
A bidiyon da alamu mutumin bahaushe ne kuma sanye yake da wasu kaya kaftan farare. A wurin an ga yadda mai saka kidan ya dinga kiran sunan uban yana kara kambama shi tare da bukatar ya cashe.
Mutane da dama sun sha mamaki kan yadda ya cire kunya a matsayinsa na dattijo ya dinga tikar rawa yadda ya ga dama.
Wasu kuma sun yaba masa kan yadda ya bayyana farincikinsa mata misaltuwa. Da alamu ba wannan bane karon sa na farko da ya yi rawa gaban jama’a ba, don babu wanda ya bayyana mamakinsa a cikin bidiyon.
Ya dade yana rawar don bidiyon ya dan yi tsawo, wanda har karkada kwankwasonsa ya dinga yi yana rawa irin na zamani. Abin dai ba a cewa komai sai wanda ya kalli bidiyon kawai
Ta Bayyana Komai: Wata Shiga Da Wata Amarya Tayi a Wajen Bikinta Ta Janyo Cece-Kuce
A cikin bidiyon mai matuƙar ɗaukat hankali, amaryar ta tsaya a gaban mutane tana yin jawabinta, yayin da angon na ta ya fito yana nuna matuƙar burge shi da tayi. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Ɗan gajeran bidiyon ya nuna lokacin da angon ya taso ya taho wajen amaryar sannan ya fara mata liƙi da maƙudan kuɗaɗe, yayin da take ta murmushi lokacin da kuɗaɗen suke hawa jikinta.
Mutane da dama sun yaba da bidiyon, sai dai abinda ya ɗauki musu hankali ba wai kuɗaɗen da aka yiwa amarya liƙi da su bane, saidai tsaɓar kyau da dirin da amaryar take da shine ya tafi da hankulan su.