By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa Alhaji Dahiru Mangal, da daukacin iyalan Mangal bisa rasuwar mahaifiyarsu Hajiya Murja Bara’u a ranar Juma’a.
Shugaban, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya bi sahun gwamnatin jihar Katsina da ‘yan asalin jihar wajen jajanta wa jagororin al’ummar yankin, wanda ya ce sadaka, karfinsa da jajircewarsa ya zama babban abin zaburarwa ga jama’a da dama, musamman mata da sauran al’ummar kasa.
Buhari ya ce an cusa sana’ar Hajiya Murja da kwazonta a cikin ‘ya’yanta da duk wadanda ta taso tsawon shekaru.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikanta ya kuma sa ta huta.