Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kare dukkan mabiya addinai da dukkan ƙabilun kasar – ko da kuwa suna da rinjaye a yankin da suke rayuwa – ko kuma tsiraru ne su, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Cikin wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai ba shugaban Najeriyar shawara kan kafofin yaɗa labarai ya fitar a jiya Lahadi, Shugaba Buhari ya mayar da martani kan rahotannin barkewar rikici a wasu sassa na kasar, rikicin da wadanda shugaban ya kira “kungiyoyi da ke da alaka da na kabilanci da na bangaranci” suke haddasa wa.
Shugaba Buhari ya gargadi irin wadannan kungiyoyin cewa gwamnatinsa ba za ta kyale su su ci gaba da rura wutar kiyayya da tashin hankali kan wasu jama’ar kasar ba.
Sanarwar ta kuma ce shugaban ya yi tir da rikce-rikicen kuma ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamantinsa za ta dauki matakan da su ka dace domin kawo karshen wadannan tashe-tashen hankulan da ke karuwa a cikin kasar.