Buhari shi ne mutum na 16 cikin jerin sunayen musulmai 500 da ke da fada a ji a duniya.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, cikin jerin masu faɗa a duniyan, Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Teyyip Erdogan shine na farko, sai Sarkin Saudi Arabia Salman Bin-Abdulaziz Saud na biyu, sa’ilin da shugaban ƙasar Iran Sayyid Ali Khameni ya zo na uku.
Shugaba Buhari, Sarkin Musulmi, Sarkin Kano na daga cikin musulmai 500 masu faɗa a ji a duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kano ya halarci bikin ƙaddamar da sabbin shugabannin Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa ta Ƙasa BON
Sunayen wadda mujallar “Persons Of The Year” dake fitowa duk shekara ta wallafa, daga cikin waɗanda sunayen su ya fita a Najeriya baya ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’adu Abubakar na III a matsayin na 19, sai Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Sheikh Ibrahim Saleh Al-Hussaini Maiduguri, da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, da Sheikh Yakubu Musa Katsina, da Sheikh Ibrahim Zakzaky, da Alhaji Aliko Dangote da dai sauran su.
A ɓangaren wasannin ƙwallon ƙafa a duniya akwai Mohammed Salah, da Sadio Mane, da Paul Pogba da Zinedine Zidane da dai sauransu.