Shugaba Buhari ya ziyarci Gidan Yarin Kuje, Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin kasar bayan harin da aka kai kurkukun ranar Talata da daddare.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan abubuwan da ya yi a ziyarar da ya kai gidan yarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Mata Biyu Sun Mutu Bayan Kifewar Jirgin Kwale-kwale A Lagas
Sai dai hukumomi sun bayyana cewa 879 ne suka tsere daga gidan yarin, bayan mutanen da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun kai masa hari.
Sanarwar da mai magana da yawun gidan-yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman fursunoni 443.
Ministan tsaron kasar ya ce akwai yiwuwar mayakan kungiyar Boko Haram 64 ne suka tsare daga gidan yarin.
Harin dai na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da ‘yan bindiga a Katsina suka yi wa kwambar motocin Shugaba Buhari kwanton-bauna a kan hanyarsu ta zuwa garin Daura