Shugaban Hukumar kula da Ma’aikatan Tsaron Ƙasar Indiya Janar Bipin Rawat an kashe shi a hatsarin jirgin sama a Kudancin Jahar na Tamil Nadu, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito.
An naɗa Rawat mai shekaru 63, na farko mai irin Wannan shekaru, a matsayin shugaban Ma’aikatan Tsaron Ƙasar a watan Janairu na shekarar 2019.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙungiyar CNG tayi Allah wadai da maganar cire tallafin Man Fetur, ta kuma yi barazanar zanga-zanga
Wannan ne ya sanya Sojojin Ƙasa, dana Ruwa dana Sama duk suka kasance a ƙarƙashin ikon Janar Rawat, kuma ya kasance yana jagorantar su.
Rundunar Sojin Saman Ƙasar ta Indiya, tace ta bada umarnin a gudanar da bincike akan hatsarin, wanda ya faru a yanayi marar kyau.
A halin yanzu Kwamitin Tsaro na gudanar da taron gaggawa akan lamarin, wanda ya samu jagorancin Babban Ministan Ƙasar Narendra Modi.