By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya kira zama da manyan jami’an tsaro daga bangarori na shugaban ma’aikata da shugaban ‘yan Sanda da sauran manyan hukumomin tsaro a fadarsa ta Villa dake Abuja .
Zaman tattaunawar ya hadar da ministan tsaro Bashir Magashi, da ministan shari’a Abubakar Malami, da ministan jin ‘yan Sanda Maigari Dingyadi, da ministan cikin gida Rauf Aregbesola da kuma ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama.
Sanarwar ta fitone daga baki mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya wallafa ashafinsa na Facebook.
Shugaban kasa Buhari ya karbi jami’an tsaro a gidan gwamnati a ranar 7 gawatan Satumba.