Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da hare-haren da jiragen yaki marasa matuka a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da suka haddasa fashewa da wata mummunar gobara a wajen babban birnin kasar Abu Dhabi.
Mutane uku ne suka mutu a lokacin da wani mummunan harin jingi maras matuki ya afkawa motocin mai a kusa da filin jirgin saman kasar da ke Abu Dhabi a ranar Litinin, wanda ya haddasa fashe-fashe da dama.
Sa’o’i kadan da faruwar lamarin, shugaban kasar ya fitar da sanarwa ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, inda ya bayyana harin a matsayin wani abin damuwa.
Buhari ya ce irin wadannan hare-haren da ake kai wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da kuma samar da ababen more rayuwa na farar hula, abin da ke haddasa asarar rayuka, abin la’akari ne daga duk wani ra’ayi mai ma’ana a fadin duniya, don haka ya kamata a dakatar da shi.
“A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, muna nuna juyayi da jaje ga jama’a da kuma kasar kawancen UAE,” in ji Buhari.
Shugaba Buhari ya bukaci a dage don ba da damar tattaunawa da alkawari.