Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban Mulkin Soja Janar Abdulsalami abubakar Mai Ritaya a fadar shugaban kasa ta Aso dake brinin tarayya.
Mai Bai waShuagab Buhari shawara kan harkar kafafen sada zumuntan zamani Bashir Ahmad shi ya bayyana haka a shafin sa na Tuwita @BashirAhmaad.
Har yanzu dai babu wani da ya ce ga abin da aka tattauna a ganawar kazalika babu wata snaarwa dangane da hakan.
To sai dai toshon Shugaban kasar yana ta nuna kaduwar shi danagane da ta’azzarar matslar tsaro a kasar.
Idan za a iya tunawa, a ranar 24 ga watan Faburairu ne Janar Abdulsalami Abubakar yain wata ziyara da Kungiyar Gwamnanonin arewa ta kai mishi ziyara zuwa gidan shi dake Minna Fadar gwmantin jihar Neja, ya bayyana cewa batun tattaunawa da yan fashin daji ba ita ce mafita ba.
“Kamata ya yi a ce hukumomin tsaro sun bullo da wasu dabarun yaki don maganace wadannan matsaloli” Cewar Abdulsalami.
Janar Abdulsalami wanda shine Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya ta Kasa ya ce yadda ake ci gaba da samun fadace-fadacecn kabilanci a kasar nan ka iya kai ta ya baro.