Allah Ya yi wa Shugaban Ma’aikatan gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, Babagana Wakil rasuwa a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli 2020.
Mai magana da yawun gwamnan Isa Gusau a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an yi jana’izar Babgana Wakil da karfe 4.00 na yamma a gidansu da ke Shehuri a garin Maiduguri.
“Allah Subhanahu wa Ta’ala, cikin rahamarsa, ya gararta masa kurakuransa ya sa shi a aljanna sannan ya ba iyalansa hakuri da danganar rashinsa.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, kamar yadda ya bayyana a cikin sanarwar.