Rundunar Sojin ƙasar nan ta bude babban sansani domin yaƙar ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Faskari na Jihar Katsina.
Yayin ƙaddamar da sansanin, Babban Hafsan rundunar sojin, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce sansanin zai mayar da hankali ne wajen yaƙar ‘yan bindiga da dangoginsu da ke addabar al’ummomin yakin Arewa.
“Za a ƙaddamar da ayyukan ɗauki a ɗaukacin sassan ƙasar nan guda shida a tare domin kyautata alaƙa tsakanin sojoji da fararen hula”, cewar Burutai.
Ya ƙara da cewa sansanin da ire-irensa a sauran yankunan na daga abubuwan da aka tsara na bikin ranar rundunar sojin ƙasar nan (NADCEL 2020) wanda ya ƙunshi fara aikin soji na musamman, ‘Exercise Sahel Sanity’, domin nuna ƙarfin rundunar na yaƙar miyagun laifuka a faɗin Najeriya.
Sai dai ya ce bikin na bana bai haɗa da ɓangaren tunawa da ‘yan mazan jiya ba saboda cutar coronavirus, amma za a yi kyakkyawan tanadin yin sa bayan lafawar cutar.