By Ishaq Dabai
Rahotanni sun bayyana cewa hoton da aka dauka daga gidan talabijin na Al-Jazeera na kasar Qatar a ranar 16 ga watan Agusta 2021, yana nuna yadda Membobin Taliban suka karbe ikon fadar shugaban kasa a Kabul bayan shugaban Afghanistan ya tashi daga kasar.
Shugabannin kasashen G20 sun amince a ranar Talata don yin aiki tare dan gujewa bala’in jin kai a Afganistan, yayin da kungiyar EU ta yi alƙawarin bada tallafin kudi Euro biliyan ɗaya kuma Italiya mai masaukin baki ta jaddada buƙatar ci gaba da hulɗa da Taliban.
Yayin da kungiyar masu kishin Islama ta fara tattaunawa kai tsaye da tawagar Amurka da Tarayyar Turai a Qatar, Shugaban Amurka Joe Biden,da Recep Tayyip Erdogan na Turkiya da Narendra Modi na Indiya sun shiga wani taron koli kan tabarbarewar rikicin tattalin arziki dana jin kai da kungiyar Taliban ta haifar a saka makon komawa kan mulki.
Kungiyar ta Tarayyar Turai ta bude tattaunawar ta hanyar yin alkawarin kudi Euro biliyan daya dai dai da (dala biliyan 1.2), gami da kudi don bukatun jin kai na gaggawa da makwabtan Afghanistan wadanda ke daukar ‘yan Afghanistan dake tserewa daga mulkin Taliban.
Draghi ya kasance yana matsa lamba don taron kungiyar G20 tun lokacin da Taliban ta kwace iko a Afghanistan a watan Agusta, yana mai cewa muhawara kan mafita dole ne ta wuce kulob din kawancen kasashen yamma.
Shugaban kasar Sin wato china Xi Jinping da shugaban Rasha Vladimir Putin basu halarci taron ba, a maimakon haka sun aika da wakilai, amma Draghi ya dage cewa dukkansu sun amince kan bukatar kara taimakawa.Dangane da taƙaitaccen bayanin da ofishin Draghi ya buga, shugabannin G20 sun nuna mahimmancin girmama haƙƙin ɗan adam da ‘yancin walwala, musamman haƙƙin mata da kuma wasu ‘yan tsiraru.
Comments 1