Jam’iyyar APC mai jagorancin kasa, ta sha alwashin fito da Dan takara nagari kuma mai farin jinin al’umma a babban zabe mai zuwa a shekarar 2023. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta
John James Akpanudoehede, Sakataren Jam’iyyar ta APC ya bayyana haka a ranar Laraba a garin Abijat.
Ya fadi hakane biyo bayan zargin da jam’iyyar adawa ta PDP ta keyi, kan cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin gadar da kujerar shugabancin Kasar nan ne.
KARANTA:- Ba ma karbar kudin kowani jarumi idan za mu saka shi a fim din Izzar so~Lawan Ahmad
James yace jam’iyyar APC tana bin tsari, ba kamar ta PDP ba, inda suka dunga gadar da kujera a tsakaninsu, hakan yayi ta faruwa a lokacin mulkinsu, ko wannan kadai zai sanya su zarge mu dayin haka.
Yanzu dai abunda mukeyi, muna kokarin tsayar da Jam’iyyar ne, ba za mu yarda wani ya kawo mana rudani karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Yace jam’iyyar APC tana kokarin zakulo mutane nagari a kowane mataki don cimma nasara a zabe mai zuwa.
Mudai yanzu kawai shirye muke mu karbi kowa, domin jam’iyyar APC ta kowane dake cikin kasar Najeriya.
Za mu tabbatar bamu bar wata kujera ba ga jam’iyyar adawa, domin kada su dunga kawo mana rudashi lokacin gudanar da mulki.
A wani labarin,
Sunday Igboho ya sharbi kuka har da majina sai kace Yaro da muka yi waya dashi, Inji Lauyansa
Jakadan Nijeriya a Benin, Janar Tukur Yusuf Buratai, yana ta kokarin ganin an dawo da Igboho da matarsa gida Najeriya.
Babban lauyan mai fafutukar kafa kasar Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun Jami’an yan sandar Jamhuriyar Benin.
Shugaban lauyoyin, Yomi Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da jaridar The Punch a daren ranar Talata.