• Gwamna El-Rufa’i ya bayyana HH Danjuna Barde a matsayin mai Samar da zaman lafiya a karamar hukumar Chikun.
• Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da tasami sahannun Mai taimakamasa kan kafofin yada labarai.
• Marigayi Dakta Barde ya mutune a safiyar jiya Laraba
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana Marigayi Sarkin Chikun Dakta Danjuna Barde a matsayin basaraken Gargajiya da ke kokarin wanzar da zaman lafiya, da kuma samar da hadin kan al’uma, wanda hakan ne ya kawo cigaba a Masarautar shi.
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a cikin sakon jaje da dauke da sahannun babban Mai taimakamas shi, a kan kafofin yada labarai Muyiwa Adekeye, ya aike wa majalissar Masarautar Chikun da kuma Iyalan Marigayi HH Dakta Barde, Wanda ya rugamu gidan gaskiya a jiya Laraba.
Gwamnan ya bayyana Dakta Barde a matsayin Mai kokarin wanzar da zaman lafiya, Wanda ya ce, duk da dumbin kalubale bai hanashi yunkurin hada kan al’uma ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba ma karbar kudin kowani jarumi idan za mu saka shi a fim din Izzar so~Lawan Ahmad
Ya Kara da cewa Dakta Barde na yin magane kawai, idan batun samar da zaman lafiya ne, da hadin kan Al’uma, da kuma cigaban su.
Malam El-Rufa’i ya kuma ce, Gwamnatin jihar Kaduna na matukar alfari da kyawawan halayen Marigayi Dakta Barde, inda kuma ya roki Ubangiji da ya jikanshi ya kuma bai wa iyalan shi, da daukacin al’umar Chikun hakuri, da Masarautar juriyar hakuri rashin da
Comments 1