Wata matashiya mai suna Poly Mukami, ta bayyana cewa tare da wani saurayi mai kuɗi lokacin farko da ta fara arba da mijinta na yanzu, mai suna John Masharia.
Poly ta amince ta auri John wanda musaki ne da baya da hannu sannan tace ko kaɗan ba tayi dana sanin yin hakan ba. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Garin neman gira: Bidiyon yadda wayar wani matashi ta faɗa ruwa yayin ɗaukar rawar TikTok
Da take tattaunawa da tashar Afrimax, matashiyar wacce ƴan’uwanta da ƙawayen suka yi adawa da auren, tace tana ganin sa ta faɗa cikin soyayyar sa.
“Lokacin farko da na gan shi, na faɗa soyayyar sa. Nayi mamaki. Na kasa yarda cewa wani zai iya amfani da ƙafafun sa yayi wasu abubuwan kamar shan shayi. Na tunkare shi domin sanin yadda yake yin hakan.”
“Mun ɗan yi hira kaɗan inda daga ƙarshe muka yi musayar lambobin waya. Ƙwarin guiwar sa ya matuƙar birge ni.”
Da aka tambaye shi game da alaƙar su, John yace ko sau ɗaya bai taɓa tambayar Poly su yi soyayya tare ba.
“Ɓan taɓa ce mata mu yi soyayya ba. Kai tsaye na gaya mata abinda nake so. Na nemi da ta aure ni kuma ta nuna a shirye take da ta bani dama ba kamar sauran ƴanmata ba waɗanda suka ƙi bani dama. Na gaya mata komai dangane da rayuwa ta kuma ba ta da matsala da hakan.”
Poly ta kuma bayyana cewa saurayin ta mai kuɗi ba shi kaɗai bane wanda tayi watsi da shi daga cikin samarinta ba domin ta kasance tare da John.
Ku Daina Tatse Aljihunan Ƙawayen Ku Da Sunan Biki -Wata Budurw Ga Amare
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta caccaki amare masu tatse aljihunan ƙawayen su lokacin biki.
Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Stella Abiodun, ta koka kan wata ɗabi’a da amaren yanzƴ suka ƙirƙiro.
Budurwar ta koka yan yadda amaren yanzu suka mayar da lokutan bikin su a matsayin wata dama ta tatse aljihunan ƙawayen su