Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ziyarci wasu da suka samu raunuka a cibiyar lafiya ta tarayya dake Gusau
Dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kewayen karamar hukumar Tsafe sun dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kan babbar hanyar Futua zuwa Gusau a daren Juma’a.
A yayin gumurzun bindiga da aka dauki tsawon sa’o’i ana gwabzawa, an kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar, kuma ana cikin haka ne wasu Sojoji suka samu raunuka.
Gwamna Matawalle ya yaba da kwazon sojojin tare da yin alkawarin ci gaba da baiwa jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ake bukata.
Hare-haren na daren Juma’a a kan hanyar Futua zuwa Gusau na zuwa ne kwanaki uku bayan da rundunar ‘yan sanda ta musamman ta dakile harin da aka kai a kan titin guda tare da kashe ‘yan bindiga biyu.