Rundunar sojin Rwanda ta ce , fararen hula da dama ne suka jikkata sakamakon luguden wuta da dakarun Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suka yi a kan iyakokin kasar .
Kana rundunar ta ce ta umarci wata tawagar kwararru masu sa ido na soji, da su gudanar da bincike na gaggawa kan lamarin .
Fargaba tsakanin kasashen biyu na cigaba da karuwa tun a watan Maris, tun bayan da Yan tawayen M23 suka farmaki Sojojin Congo a kan iyakokin kasar, Wanda Kuma Rwanda ta Karyata zargin cewa ta na Goyon Bayan Yan awaren.
Rahotanni sun nuna cewa, kungiyar Yan tawayen sun karbe Iko da wani yanki dake Gabashin DR Congo yayin Wani artabu a shekarar 2012 zuwa 2013
Rayhaan Radio ya gano cewa, mutane da dama sun bar gidajen su dake Lardin Kivu na Arewacin Congo inda sun kayi sansanin a birnin Bunagana na kasar Uganda.
Kazalika Shugaban hukumar kula da Yan gudun hijira na majalissar Dinkin duniya a Uganda Joel Boutroue ya bayyanawa kafar yada labarai ta BBC cewa, dubban Yan gudun Hira sun isa Uganda a jiya Litinin.
A wani labarin Kuma na daban.
Jami’ar Ekiti ta cire kan ta daga yajin aikin ASUU, ta sanar da ranar cigaba da Karatu
Jami’ar Jahar Ekiti dake Ado-Ekiti (EKSU) ya sanar da cewa harkokin Karatu zai cigaba a ranar Talata 24 ga watan Mayu.
Bode Olofinmuagun Daraktan kula da Harkokin Al’umma ya sanar da hakan a ranar Litinin.
Yanke hukuncin ya biyo bayan wani taro da aka gudanar a ranar Litinin.
Olofinmuagun yace tattauna matsalolin da yajin aikin ASUU ya haifar ga dukkanin Ƙungiyoyin guda huɗu.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta fara yajin aiki a ranar Fabrairu na Shekarar 2022.
Mai Magana da Yawun Jami’ar yace Shuwagabancin Makarantar yana sane da irin baƙin ciki da Ɗalibai da Iyaye ke fuskanta.
Ya bayyana cewa har yanzu zangon Karatu na (2021/2022) ba a kaiga fara shi ba, a yayinda har yanzu Samista ta biyu a zangon Karatu na 2020/2021 ba’a kammala shi ba.
Haka zalika nan da wani lokaci za’a fara ɗibar Ɗalibai zuwa ga Zangon Karatu na Shekarar 2022/2023.
Yace Makarantar ta bude Makarantar ne domin Ɗalibai, Iyaye, Al’umma da kuma ɗorewar Cigaban ta.