By Abbas Yakubu Yaura
Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, kuma kwamishinan gudanarwa, Dr Kenneth Ugbala, ya yi murabus daga mukamin sa don cim ma burinsa na tsayawa takarar Sanata.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Alhamis bayan wata tattaunawa ta sirri da kwamitin aiki na jam’iyyar APC ta Ebonyi a sakatariyar jam’iyyar da ke Abakaliki.
DUBA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Buhari Ya Gana Da Gowon, Abdulsalami, Jonathan A Fadar Shugaban Kasa Dake Abuja
Ugbala ya kuma bayyana cewa ya yi watsi da kudirinsa na tsayawa takarar gwamna ne saboda muradin jam’iyyar da kuma neman wakiltar mazabar Ebonyi ta tsakiya.
A cewarsa: “Na zo nan ne domin in tuntubi kwamitin gudanarwa na jam’iyyarmu na Jiha da kuma neman amincewarsu da goyon bayansu, domin tsayawa takarar Sanata, a zabe mai zuwa na 2022/2023 na yankin Ebonyi ta tsakiya.
“Kun san jam’iyyar siyasa wata kafa ce da za ku iya shiga cikin shugabanci. Kuma kafin a dauki kowane mataki, ya zama dole a tuntubi shugabannin jam’iyyar don neman amincewarsu. Shi ya sa nake nan,” inji shi.
Ugbala, wanda ya taba zama babban mataimaki na musamman (SSA) kuma kwamishina a gwamnatin Gwamna David Umahi, kafin hawansa mukamin Sakataren Gwamnatin Jiha, ya ce zai tabbatar da wakilci mai inganci idan aka zabe shi Sanata.
Ya ce: “Na tsaya takara ne domin in ba da gudummawar kaso na domin samun wakilci mai inganci da tabbatar da bin doka da oda, da kuma hada kai da sauran shugabannin da Jihar ke dorawa kan karagar mulki a zaben dake tafe na 2023, don ganin mun gina tare da fadada ayyukan da Gwamna mai ci ya yi. .
“Na ba da kaina don wannan aikin don amfanin talakawa.”
Akan murabus dinsa, Ugbala, ya ce ya na da cikakkiyar masaniya kan sabuwar dokar zabe, kuma ya dauki dukkan matakan da suka dace domin bin ta, ciki har da mika takardar murabus dinsa ga hukumomin da suka dace.”
Comments 1