Wata matar aure ta koka kan yadda mahaifiyar mijinta take hanata sakewa a gidan aurenta.
Matar aure wacce ta nemi da a sakaya sunanta, ta bayyana matsalolin da take fuskanta ne dai a wata wasiƙa da ta rubutowa shafin haɗa aure na Northern Hibiscuss a shafin Facebook.
KU KARANTA KUMA: ZAC Zamfara Sun Fara Binciken ‘Yan Kasuwar Da Suka Ki Karbar Tsoffin Kudi
Matar auren ta bayyana cewa a gida ɗaya suke tare da ita da surikar ta, kuma duk wata kyautatawa da ƴa yakamata ta yiwa mahaifiyarta, tana yi mata tunda ta ɗauke ta kamar ita ta haifeta.
Tace mijinta na matuƙar son ta da nuna mata kulawa, wanda hakan ne ya sanya mahaifiyar sa take cewa ta mallake mata ɗa.
Ta bayyana cewa ko kaɗan bata bari su mori rayuwar aure ita da mijinta, domin sai suna cikin raya sunnah zata aiko jikarta ta buga musu kofa, tana son ganin mijin ciwon hawan jininta ya tashi, kuma idan ya tafi bata bari ya dawo sai safiya.
Tace mahaifiyar na ƙorafin cewa ta cika jaraba saboda haka ba zata bari ta tsofar mata da ɗa.
Daga ƙarshe dai sai da ta kai cewa idan suka samu suka raya sunnah, sai dai ta shimfiɗa masa tabarma yayi wankan Sallah a ɗaki domin kada mahaifiyar ta san halin da ake ciki.
Matar auren ta koka kan wannan takura da surikarta take yi mata, domin ta hana ta more rayuwar aure ita mijinta, waɗanda su duka biyun suna cikin takura kan wannan halin na mahaifiyar sa.
Tirƙashi: An Ritsa Fasto Ɗauke Da Kororon Roba Yana Tsaka Da Wa’azi
A wani labarin na daban kuma, an ritsa fasto ɗauke da tulin kororon roba yana tsaka da wa’azi.
Wani bidiyo ya da aka ɗauka ya nuna yadda mutane suka cika da mamaki bayan ganin wani fasto mai wa’azi ɗauke da kororon roba.
Faston wanda yake iƙirarin cewa shi mutumin ƙwarai ne, ya nemi mutanen dake kan layin cirar kuɗi a ATM su bari ya fara cire kuɗi duk da akwai waɗanda suka riga shi.