Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci Unguwar kofar Mazugal, Lungun mai Lalle, don jajantawa waɗanda iftila’in rusau ya afkawa a cikin makon nan.
Gwamnan na Kano wanda mataimakinsa Alhaji Nasir Yusuf Gawuna ya wakilta ya ce haƙiƙa wannan al’amari abin jajantawa ne.
Mutane goma sha takwas ne dai iftilai’n na rusau ya afkawa inda kuma yara biyu suka rasa rayukansu a Unguwar ta Kofar Mazugal, Lungun mai Lalle.
https://dimokuradiyya.com.ng/wani-ginin-bene-ya-rufta-tare-da-hallaka-mutane-2-a-jihar-kano/
Da yake jawabi yayin ziyarar kwamandan hukumar Hizba ta Jihar Kano Sheikh Harun Ibn Sina, ya buƙaci mutanen su ɗauki wannan lamari tamkar jarrabawa daga ubangiji, tare da addu’a ga mamatan da suka rasu.
Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, inda kuma aka kai kayan abinci da kuɗi da kuma kayan gini.