Wani ƙayataccen bidiyo da aka sanya a yanar gizo ya nuna wani ango cikin ƙasaita yana nuna tsantar ƙaunar da yake yiwa kyakkyawar amaryar sa.
A cikin bidiyon mai matuƙar ɗaukat hankali, amaryar ta tsaya a gaban mutane tana yin jawabinta, yayin da angon na ta ya fito yana nuna matuƙar burge shi da tayi. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Ƴan ta’addan ISWAP sun yi rabon tsofaffin kuɗi a Borno.
Ɗan gajeran bidiyon ya nuna lokacin da angon ya taso ya taho wajen amaryar sannan ya fara mata liƙi da maƙudan kuɗaɗe, yayin da take ta murmushi lokacin da kuɗaɗen suke hawa jikinta.
Mutane da dama sun yaba da bidiyon, sai dai abinda ya ɗauki musu hankali ba wai kuɗaɗen da aka yiwa amarya liƙi da su bane, saidai tsaɓar kyau da dirin da amaryar take da shine ya tafi da hankulan su.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@damien65 ya rubuta:
“Idan da ace ina da irin wannan a gidana, ba zan taɓa cin amanar matata ba.”
khadee100 ta rubuta:
“Ta zo ta gama nunawa duniya kanta. Wasu mazan basu da kishi gaskiya.”
@mnenajnifa ya rubuta:
“aa aa kalli diri wannan juyawar da tayi bayan ta gama jawabi. Wajen ya burgeni.”
@199abi ya rubuta:
“Wai a ina suke samun irin waɗannan matan ne, ina buƙatar ɗaya da gaggawa.”
@huawabello ta rubuta:
“Wannan budurwar ƴar Arewacin Najeriya ta haɗa komai.”
@beffjezos25 ya rubuta:
“A matsayina na Inyamuri, shin zan iya auren Bahaushiya? Maganar gaskiya ina son yanayin su sannan waɗannan matan akwai ɗan karen kyau.”
Rahama Sadau Tayi Muhimmin Kira Ga Gwamnatin Tarayya Kan Masana’antar Finafinai
A wani labarin na daban kuma, jarumar finafinai Rahama Sadau ta nemi gwamnatin tarayya da ta waiwayo masana’antar finafinai.
Shahararriyar jaruma kuma furodusa, Rahama Sadau, tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta narka kuɗi kan harkar finafinai, inda take cewa rashin isassun kuɗi na kawo naƙasu wajen yin finafinai masu inganci a Nollywood.
Majiyar mu ta rahoto cewa jarumar tayi wannan furucin ne a birniɓ tarayya Abuja, a wajen haska wani sabon fim ɗin ta mai suna ‘The Plan’.