Ahmad Isah wanda akafi sani da Ordinary President, mai gidan Rediyon Brekete Family dake Abuja, yace Abba Kyari jarumi ne kuma zakakurin Dan sanda, yayi ayyukan yabawa sosai a kasar nan. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
A halin yanzu dai an dakatar da Abba Kyari bisa laifin da ake zarginsa dashi na karbar cin hanci daga Ramon Abbas.
Ramon Abbas wanda akafi sani da Hushpupi, ya kasance dai kasurgumin dan damfara ne da yayi kaurin suna a duniya, an dai ruwaito ya baiwa Abba Kyari cin hanci dala miliyan daya kan ya kama wani da ya ci amanarsa.
KARANTA:- Har’ila Yau dai Sanata Uba Sani a majalisar dattijan Nageriya
Ordinary President, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gidan Rediyonsa, yace Kasar America bata kyauta ba da dake tuhumar Abba Kyari.
Kamar yadda ya fada “Wannan yanayin da Abba Kyari ya shiga, wadansu daga cikin Yan sanda suna murna, wadansu kuma suna ta gulma.”
“Kunata murna kuna jindadi, to bari na gaya maku, ko kun ki, ko ku so, da yardar Allah Abba Kyari ba zai tozarta ba, ayyukan da yayi a kasar nan yafi karfin a tozartashi koda zargin da ake masa ya zama gaskiya.”
“Kasar America ba ta isa ta gaya mana yadda za muyi rayuwa ba, America ba Aljannah bace, da akwai Yan shaye-shaye a America, akwai mazunata, akwai masu garkuwa da mutane, akwai Yan ta’adda daban-daban, me America za ta nunama kasashen Africa in banda rashin shugabanci na gari.”
“Muna tare da Abba Kyari, Kuma In Shaa Allah, Allah zai tsare mana shi.”
“Da yardar Allah wata rana Abba Kyari sai ya zama shugaban rundunar Yan sanda Nigeria, suna kawai bakin ciki dashi ne saboda irin nasarorin da yake samu, ba za su iya yin rabin abunda yake yi ba, Abba Kyari ya ruga ya wuce da tunanin su, Dan sanda ne jarumi haziqi ba wai bawa ba.”