Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana amannarsa wajen cewa tarihi zai musu adalci domin sanya su cikin wadanda zai dinga tunawa da su, musamman idan aka yi duba dangane da tarihin yadda suka gaji kasar.
Shugaba Buhari a cewarsa wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Femi adesina ya fitar, jamiyyar APC ta samu mulkin kasar nan a lokacin da take cikin yanayi na fama da matsalar tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arziki.
KU KARANTA: Aikin Layin Dogon Najeriya Zuwa Nijar Babbar Dama Ce Ga Kasashen – Sambo
Shugaba Buhari yayin ziyarar kaddamar da wasu ayyuka da yake yanzu haka a jihar Katsina gwamnatinsa tayi iya abinda zasu iya wajen samar da sassauci dangane da hain da suka samu kasar.
Daily Trust ta rawaito cewa Daga nan sai ya yabawa gwamna Aminu Masari bias yadda ya samar da managartan ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta samar a jihar, wanda yace yana da tabbacin alummah zasu amfana da su matuka.
A yayin ziyarar shugaban kasar a jihar Katsina ya kaddamar da wasu ayyuka da suka hadar da babban asibitin jihar, sai kuma wata gadar sama ta farko wadda itama gwamna Masari ya samar da ita, wadda yanzu haka ta kamala da kusan kaso 90.
Wani labarin kuma: Sojoji Sun Lalata Haramtattun Matatun Mai 39, Sun Kama Barayin Da Suke Barnar
Shedikwatar tsaro ta ce dakarun hadin gwiwa na Operation Delta Safe, sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur 39 a yankin Kudu maso Kudu cikin makonni biyu da suka gabata.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo janaral Musa Danmadami, ya bayyana haka a wani taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis din nan a Abuja.