A yayin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Osun ke yanke hukunci a yau, an tsaurara jami’an tsaro da dama a harabar babbar kotun da ke Osogbo da kewaye ,Vanguard ta rawaito.
Tsohon gwamna Adegboyega Oyetola ya kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli inda ya ce an tafka kura-kurai tare da nuna shakku kan cancantar Gwamna Ademola Adeleke na tsayawa takarar zaben.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tabbas Tarihi Ba Zai Manta Da Gudunmawar Dana Baiwa Najeriya Ba – Buhari
Bangarorin zaben da ake takaddama a kai sun yi jawabi tare da amincewa da rubutattun adireshi na karshe a gaban kotun a ranar 13 ga watan Janairu bayan da suka gabatar da baje kolin shaidu yayin shari’ar.
Yayin da kwamitin mai shari’a Tertse Kume ke yanke hukunci a yau, an jibge jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a fadin babban birnin jihar.
Harabar kotun dai ta kasance tare da hadin gwiwar jami’an rundunar ‘yan sanda, DSS, jami’an tsaron farin kaya, NSCDC.
Ma’aikatan shari’a a kotun sun sha wahala wajen shiga kotun yayin da jami’an tsaro suka dage a kan tantance masu ziyara a harabar.
Haka kuma, an jibge jami’an tsaro a ofishin yakin neman zaben Tinubu-Shettima, sakatariyar APC, gidan Imole da sauran muhimman wurare da suka hada da mahadar Oke-Fia, Lamenco da Olaiya.
Duk magoya bayan APC da PDP ba a ba su izinin shiga ba kamar yadda suka saba yayin da aka yi wa wadanda aka ba su damar shiga kotu binciken kwakwaf.
A wani labarin kuma, Aikin Layin Dogon Najeriya Zuwa Nijar Babbar Dama Ce Ga Kasashen – Sambo
Gwamnatin tarayya ta ce aikin layin dogo da ake kokarin samarwa daga nan Najeriya zuwa Jamhuriyar Nijar zai taimaka wajen bunkasa kasuwanci da harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Daraktan yada labarai na maaikatar sufuri ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar tare da rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja.