A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a kasashe da dama a fadin duniya kawo yanzu ya yi tafiye-tafiye har sau 51 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015, Vanguard ta rawaito.
Ministan harkokin wajen kasar Mista Geoffrey Onyeama, a ranar Alhamis,yana mai jaddada cewa tafiye-tafiyen da shugaba Buhari yayi ba su isa ba idan aka yi la’akari da yadda aka gudanar da taron matakin tuntubar da shugaban kasa ya kamata yayi da takwarorinsa domin amfanin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: U-20 AFCON: Young Chipolopolo Ta Zambia Sun Isa Abuja Domin Buga Wasan Sada Zumunci Da Flying Eagles
Onyeama wanda ke bayar da katin shaidar ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Buhari tun daga shekarar 2015 zuwa yau, ya bayyana cewa Buhari na bukatar karin tafiye-tafiye a cikin wannan lokaci duba da irin yawan tuntubar da ofishinsa ke bukata a matsayinsa na daya daga cikin masu kula da harkokin kasashen wajen Najeriya.
Onyeama, yayin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, ya yi nuni da cewa bai yi mamakin ikirari da wasu ‘yan Najeriya ke yi na cewa Buhari ya yawaita tafiye-tafiye ba, yana mai cewa masu wannan ikirari ba su fahimci muhimmancin tafiye-tafiyensa ga Najeriya da ‘yan kasar ba. .
Ministan ya ce, “Ba gaskiya ba ne tafiye-tafiyen da Buhari ya yi a kasashen waje sun yi yawa. Ba zan yarda da wannan ikirari ba. Zan iya cewa bai isa ba. Ba za ka iya tunanin abin da ya cimma da abin da yake yi tare da mu’amalarsa ta kashin kai tsakaninsa da takwarorinsa na kasashen waje ba.
Buhari shi ne ministan harkokin waje na daya a Najeriya kuma idan na samu hanya zan ce ya ma kara tafiye-tafiye zuwa kasashe da dama domin kamar yadda na fada a baya Buhari shi ne shugaban da ya fi kowa a kasar nan.
“Ban yi mamaki ba domin akwai wani karin magana da ke cewa ba a girmama annabi a kasarsa. Idan ka san irin soyayya da mutunta Buhari da wasu shugabannin duniya suke yi, abin burgewa ne idan kana nan sai ka ga hakan kuma sau da yawa sukan dage shi zuwa ko da ya ce ba zai yiwu ya zo ba. ” in ji Onyeama.
Ministan ya yi alfahari da cewa huldar da Buhari ya yi da shugabannin kasashen waje tare da manufofin diflomasiyya na Najeriya ya jawo jarin waje da dama a Najeriya, sai dai ya ce ba zai taba yiwuwa ma’aikatarsa ta sanya darajar kudi ga irin wadannan jarin ba kamar yadda ake yi a yau.
Dangane da yadda wasu kasashe ke musgunawa ‘yan Najeriya, ministan ya nuna takaicinsa kan wannan ci gaba, inda ya ce ma’aikatar ta sha yin taka-tsan-tsan wajen kubutar da dubban ‘yan Najeriya da suka makale a kasashen ketare sakamakon cin zarafinsu.
Sai dai ministan ya yi gargadin cewa tun da Najeriya ba za ta iya hana ‘yan Najeriya tafiye-tafiye zuwa kasashen da suke so ba, ya kamata ‘yan Najeriya su koyi kame kansu daga ayyukan da ke janyo raini da kunya daga kasashen waje akai-akai.
A wani labarin kuma, Matata Ba Ta Da Tausayi, Ta Kashe Danta Na Farko — Wani Maigida Ya Shaidawa Kotu
Wata kotun Kwastamare dake zamanta a Ado-Ekiti ta raba auren shekaru 23 da aka yi tsakanin Isiaka Odeyemi da matarsa, Feyisola Olapeju.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa an raba auren ne a bisa dalilin fadan da ya kaure da alaka da barazanar da matar ta yi da layoyi da kuma rashin kwanciyar hankali da matar ta ke haifarwa.