Wata budurwa wacce bata da hannuwa ta karaɗe yanar gizo saboda biyayya da kulawarta ga mijinta.
A wani bidiyo da aka sanya a TikTok, an nuna budurwar na wani mutum wanda ake kyautata zaton cewa mijinta ne. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Bidiyon ya fara ne da nuna budurwar riƙe da ruwa domin mutumin ya wanke hannuwan sa.
KU KARANTA KUMA: Sababbin kuɗi: Wata mata mai juna biyu ta mutu bayan mijinta ya kasa ciro kuɗi a banki
Alamu sun nuna cewa ya kammala cin abinci ne inda ta ce bari ta zuba masa ruwa ya wanke hannun sa.
Tayi amfani da wuyanta tare da kuncinta wajen gyara zaman kofin bayan ta riƙe shi da hannunta na hagu wanda yake a gundile. Hannunta na dama shi ma a haka yake a gundile.
Amma gwanin ban mamaki, tayi amfani da su ta tattara kwanukan bayan ya kammala cin abincin.
Jajircewarta da biyayyarta ga mijin nata duk da halin da take ciki ya sanya mutane da dama sun yaba mata.
Yanayin rayuwarta ya burge mutane waɗanda suka ce halin da take ciki bai sanya ta ƙi yin farin ciki a rayuwarta ba. Wani mai amfani da @user7039992739787 shine ya sanya bidiyon.
Ku kalli bidiyon a nan
Wata Mata Ta Mayar Da Ƴar Tsana Jika Bayan Ƴarta Ta Ƙi Haiho Mata Jika
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta nemi mafita bayan ƴarta ta ƙi haiho mata jika.
Wata budurwa a yanar gizo ta nuna bidiyon yadda mahaifiyarta take kulawa da wata ƴar tsana da ta siyowa kanta.
A cewar budurwar, mahaifiyarta ta samo ƴar tsanar ne domin har yanzu ta ƙi yarda ta haifo mata jika.
A bidiyon da aka sanya a manhajar TikTok, an nuna mahaifiyar ta na sanyawa ƴar tsanan mara gashi a kai kayan sanyawa kamar wani yaro na gaske, sannan ta nuna bata damu da bidiyon da ƴar ta ke ɗaukarta ba.