By Abbas Yakubu Yaura
Uwargidan gwamnan jihar Oyo, Misis Tamunomini Makinde, tace rashin ayyukan yi da tabarbarewar tattalin arzikin ke haifarwa ba hujja ce ba ga kowane namiji ya tayar da hankalin matarsa ko kuma wata mace.
Domin isar da sakon, uwargidan gwamnan ta jagoranci matan shugabannin kananan hukumomi da sauran masu rike da mukaman gwamnati a jihar kan yakin cin zarafin mata da ‘yan mata.
A zantawar da ta yi da wakilinmu a wajen tattakin gangamin, Makinde tace ya kamata mata su rika tofa albarkacin bakinsu kan duk wani nau’in cin zarafi da ake yi musu.
Sannan tace, “Wasu mutane sun rasa ayyukansu sakamakon COVID-19 kuma sun yi takaici saboda hakan,a matsayinsu na maza, suna tunanin yadda zasu ciyar da iyalansu, amma wannan ba uzuri bane ka dora hannunka akan matarka, Ba abin yarda ba ne kuma dole a daina.”
Da take jawabi yayin tattakin a unguwar Agodi dake Ibadan, ta kuma koka kan yadda ake lalata kananan yara.Tace kin yin magana da masu ruwa da tsaki suka yi shi ya sa aka ci gaba da aikata laifin.
“Kada ku bar kananan yara ba tare da kulawa ba, kuma kada a yi wa ‘yan matanmu aikin yara, jima’i ko cin zarafi,” in ji ta.