Shugaban Madagascar ya sanar da cewa kasarsa za ta fara gwajin maganin rigakafi da ruwan ganyen tazargade domin warkar da cutar korona.
Andry Rajoelina ya ce a mako mai zuwa za a fara gwajin. Ya bukaci al’ummar kasar su shuka itacen tazargade. Shugaba Rajoelina ya ce yana tattaunawa da masana kimiya a Amurka domin taimakawa wajen binciken.
Shugaban kuma ya ce yana kokarin tabbatar da maganin daga Hukumar Lafiya ta Duniya.