Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sen. Iyiola Omisore, a ranar Litinin, ya ce babu wani zabi ga yan Najeriya a zaben shugaban kasa, illa su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki Sanata Bola Tinubu.
Omisore ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da wasu shugabannin jam’iyyar a sakatariyar APC da ke Legas.
KARANTA ANAN: Na Fita Daga NNPP — Shekarau Ya Zargi Kwankwaso Da Wulakantashi
Sakataren jam’iyyar APC, wanda ya tafi gabanin kammala taron, ya bukaci ‘yan jam’iyyar da al’ummar shiyyar Kudu maso Yamma da su tashi tsaye su hada kai domin ganin Tinubu ya zama shugaban kasar Nijeriya na gaba.
Ya kuma bukaci al’ummar yankin Kudu maso Yamma da ‘yan Najeriya da su guji yaudara, yana mai jaddada cewa yaudara karshen ta dana sani ce.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa sakataren ya ce taron an sanar da shi ne a kan bukatar shirya dabarun tunkarar zaben 2023.
Omisore ya ce jam’iyyar ta kudiri aniyar nuna nasarori da karfin da Tinubu ya samu a cikin shekaru 20 da suka gabata kuma za ta yi iya kokarinta wajen ganin ta sayar da dan takararta tare da gyara wasu labaran karya da kura-kurai a waje.
Sakataren jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa, Tinubu ya yi ayyuka da dama wajen ciyar da jihar Legas gaba ta kowace fuska kuma ya cancanci a zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.
A wani labarin kuma: Majalisar Dokokin Kano ta amince da sabbin kwamishinonin Ganduje
Majalisar Kano Ta Amince Sa Sabbin Kwamishinonin Ganduje
A ranar Litinin ne majalisar dokokin jihar Kano ta tantance sabbin kwamishinoni guda tara da gwamna Abdullahi Ganduje ya nada.
Kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim-Chidari ne ya sanar da karbar wasikar da Ganduje ya aika wa Majalissar na karin wanj kwamishina guda mai suna Aminu Ibrahim-Tsanyawa.