Tinubu ya gana da Ganduje, ɗan takarar gwamnan Kano
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tawagar jam’iyyar APC daga jihar Kano a ranar Alhamis.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci tawagar zuwa taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Jigawa ta biya kuɗin fansho da garatuti
Taron ya kuma samu halartar dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Kano a 2023, Nasiru Gawuna.
Mako guda kenan da kotun koli ta tabbatar da Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP a matsayin gwamnan jihar Kano.
A watan Maris ne mulki ya sauya daga jam’iyyar APC a lokacin da Gawuna ya samu kuri’u 890,705 bayan Yusuf wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana wanda ya lashe zaben da kuri’u 1,019,602.
Amma, Gawuna ya ki amincewa da sakamakon a kotu wanda ya kai ga kotun daukaka kara ta ayyana shi a matsayin gwamna.
A ranar 12 ga watan Janairu ne kotun koli ta mayar da Yusuf a matsayin gwamna.
A wani labarin kuma:Wike ya gargaɗi ƴan siyasa da kada su kawo masa cikas a aikinsa
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin ba zai yi wasa da ‘yan siyasa da ke kawo cikas ga ayyukan gwamnati da ke gudana ba.
Wike ya ce manufarsa ita ce kare muradun jama’a ba wai tausasa son zuciya na ‘yan siyasa ba.