Wike ya gargaɗi ƴan siyasa da kada su kawo masa cikas a aikinsa
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sha alwashin ba zai yi wasa da ‘yan siyasa da ke kawo cikas ga ayyukan gwamnati da ke gudana ba.
Wike ya ce manufarsa ita ce kare muradun jama’a ba wai tausasa son zuciya na ‘yan siyasa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mun mayar da hedikwata zuwa Legas ne don amfanin ƴan Najeriya – FAAN
Ya yi magana ne a lokacin da ya koka kan matakin da wani dan majalisar wakilai ya dauka na kawo cikas ga wani aiki da ake yi a gundumar Guzape da ke babban birnin tarayya Abuja, saboda wata riba ta kashin kai.
Yayin da yake duba wasu ayyukan tituna da ke gudana a Guzape Lot 2, wanda Gilmour Construction ke gudanar da shi, da Tituna B6 da D12 a kan titin Constitution Avenue, wanda Julius Berger Construction ke gudanarwa, Wike ya ce dan majalisar ya ba da umarnin dakatar da aikin ba tare da bin ka’ida ba.
“Ba za mu dauki shi da wasa ba. Wannan ba aikin sirri bane; aiki ne na jama’a, wanda hukumar babban birnin tarayya ke gudanarwa.
“Idan akwai wani koke, muna ganin duk wanda ke da hannu a kai ya kai kararmu, kada ya je ya yi amfani da ‘yan sanda ya hana wani halaltaccen kamfani yin gine-ginen jama’a, wanda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi.
“Mun umurci dan kwangilar da ya koma don tabbatar da cewa ba su kula da abin da ake kira dakatarwa ba. Dole ne su koma su kammala aikin, wanda muke sa ran cewa shugaban zai kaddamar a watan Mayu, “in ji Wike
A wani labarin kuma:Gwamnatin Jigawa ta biya kuɗin fansho da garatuti
A karshe dai masu ritaya a jihar Jigawa suna cigaba da farin ciki bayan sun karbi alawus dinsu na ritaya.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa shirin bayar da gudunmawar fansho na jihar Jigawa da na kananan hukumomin jihar ya kasa biyan kudin gratuti da na ritaya na tsawon watanni sakamakon wasu matsaloli da suka jefa shirin cikin damuwa.