Jigo a Jam’iyar APC Mai Mulki Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana godiyar sa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa ziyar da ya kai mishi a birnin London a ranar 12 ga watan Ogustan shekarar nan da muke ciki.
A cikin wata sanar wa da Ofishin kula da harkokin kafafen yada labarai na Tinubu ya fitar a jiya juma’a ya ce, “Ziyar ta abokantaka ce, indaya Kara da cewa, “Na tarbi Mai mutumci, da kuma kula wa da mu, wato Shugaban kasar mu”.
“Wannan karamci ne Shugaban kasa ya sake nuna wa, game da irin tunanin sa, da tawali’un sa, sannan kuma ya bijire wa sukar, da wasu masu sukar shi su ke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya jajanta wa takwaran shi na Jamhoriyar Niger
Kazalika , Asiwaju ya yaba wa Shugaban kasa Buhari, na yin amfani da lokacin shi, wajan ziyartar shi, inda kuma ya yi wa Shugaban fatan ci gaba da samun nasara a gwamnatin sa, da kuma jagorantan kasar nan bisa turba da ya dace.
A wani labarin Kuma
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, yace kowane Ma’aikacin Gwamnatin Tarayya, ya cancanta ya Mallaki Gida, a saboda Haka akwai bukatar yin gyare-gyare a aikin Gwamnati a Nigeria.
Mai Magana da Yawun Osinbajo Laolu Akande, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, inda yace Mataimakin Shugaban Kasar yayi magana ne, bayan ya karbi jawabi akan shirin bullo da Sabbin Dubaru a bangaren aikin Gwamnatin Tarayya na Shekarar 2021-2025 a Villa dake Abuja.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Dr Folasade Yemi-Esan ta yiwa Mataimakin Shugaban Kasar jawabi.
Taron dai an gudanar dashi ne a matakin Tarayya, Wanda dama yin gyare-gyaren tuni ana kan hanyar gudanar dashi tun Shekarar 2017.
Yin gyare-gyaren dai, Kwamitin Kaddamar da Shirin, Wanda ya kunshi Mambobi da aka zabo daga bangaren Gwamnati da Wanda bana Gwamnati ba, tare da Kungiyoyin bada agaji suka Jagoranta.
Acewar Osinbajo, akwai bukatar ayi wani abu mai ma’ana Kuma babba dazai kawo canje-canje.
“Ina tunanin ya kamata ace munyi wani abu babba dazai kawo canji mai ma’ana, domin magance wasu al’amurra musamman bangaren wuraren zama ga Ma’aikatan Gwamnati.
“Zamu iya yin gidaje da yawa; Muna tunanin Gina gida Dubu Dari 300,000 a Karkashin Shirin tattalin arziki wato-ESP.
“Babban Bankin Nigeria ya ware Naira Biliyan 200, amma munga cewa zamu iya Gina gidaje da yawa, Kuma zamu iya sanya Ma’aikatan Gwamnati su zama, su zasu amfana da Shirin yin gidajen.”