Kwamitin Asusun Gwamnati na majalisar Dattijai ya gayyaci Kamfanin Kula da Man Fetur na Kasa NNPC da ya gurfana a gaban shi ya yi bayani dalla-dalla kan inda Naira Tiriliyan hudu da digo sufuli bakwai ya shiga daga shekarar 2010 zuwa 2016.
Sai dai kamfanin ya bayyana ne gaban majalisar ana makon karshe da fara gudanar da wannan bincike don fayyace ina aka kai wannan kudi har sama da Naira tiriliyan hudu.
Kazalika Kamfanin ya rubuta wata takarda don ta inda ya ce an yi amfani da kudaden ne wajen gyara bututan mai da harkar cire tallafin mai da kuma matsalar tsaro gami da wasu harkokin da ya shafai hukumar gudanrwar kamfanin
Amma fa bisa ga dukkan alamu Kwamitin majalisar bai gamsu da wadannan hujjoji ba inda ya bukaci kamfani da ya kawo bayanai dalla-dalla a rubuce wanda hakan ne kawai zai sa ya janye wannan tuhuma.
Ko da yake dai kamfanin ya mika muhimman takardu dake dauke da bayanan yadda aka yi amfani da kudaden, to amma shugaban Kwamitin Majalisar Sanata Mathew Urhoghide ya fada wa mambobin majalisar cewa hakan bai wadatar ba, dole ne sai kamfanin ya gurfana a gaban shi.
Ya ce ba za a yi musu rufa ido ba, don haka sai kamfanin ya yi zo ya kare wdannan takardu da ya mikabaki da baki.
Ya ce “Mun baiwa NNPC wa’adi zuwa ranar Laraba ko kuma mun gama daga mishi kafa kenan zuwa alhamis da ya gurfana a gaban mu.