Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila wadda take fafata gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila ta nuna sha’awar ta ta sayen shahararren ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Madrid wato Saul Niguez domin dawo dashi gasar Firimiya.
Kafin Tottenham ta nemeshi tuni ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama musamman daga ƙasar ta Ingila suke nemansa da suka haɗar da Manchester United da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal dake birnin London na ƙasar Ingila amma kuma haƙansu bai cimma ruwa ba.
Sai dai akwai alamun ita Tottenham ta matsa sosai wajen sayensa duba da irin gudun mawar da yake bayar wa a ƙungiyar ta Athletico Madrid musamman wajen jefa ƙwallaye na bajinta.
Mai horas da Tottenham wato José Mourinho da ake kira da The Special One shine ya nuna cewar tabbas idan aka sayi Saul Niguez to zai baiwa Tottenham gudun mawa sosai kamar yadda ya kamata.
Tottenham dai bazata sami damar buga gasar zakarun nahiyar turai ba a kakar wasa mai kamawa ta 2020 zuwa 2021 amma zata buga gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai da ake kira da Europa League.