Kungiyar yan Tifa ta ce za ta kara kudi kan yadda take sayar da yashi da dutse da kuma kasa, sakamakon karuwar kudin Man diesel da suke amfani da shi, a motocin su wajen jigilar.
Shugaban kungiyar Maamun Ibrahim Takai ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce a baya sunyi nufin tafiya yajin aiki ne kan matsalar Amma daga baya suka fuskanci gara suyi Karin kudin.
Ya ce a da suna sayan Lita daya ta Man diesel akan Naira 200 zuwa naira 250, Amma yanzu ya Kai Naira 700 kan kowacce Lita.
Haka kuma ya ce akwai wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da suke amfani da su a jikin motocinsu da aka karawa kudi da kusan kaso 400 cikin Dari, tare da cewa Karin farashin zai fara ne nan take.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hauhawar farashin kayan ginin dai na ci gaba da dagawa jama’a hankali, sakamakon yadda siyan kayan ke neman gagarar Talaka.
A kwanakin baya dai an samu hauhawar farashin siminti Inda ya tashi daga N3,700 zuwa kusam N5,000, yayin shima bulon gini ya karu, daga Naira 140 zuwa Naira 200, a wasu wuraren ma har ya Kai Naira 250.