Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya yi karin haske kan shirin yi wa malamai rajista na Biometric a jihar.
A cewar gwamnan, wannan aikin gwaji ba wai an bujiro da shi don korar wani malami ba ne, sai dai don sanin hakikanin adadin malaman da suke aiki.
Tambuwal ya ce wannan bayanin ya zama dole domin ta haka ne za a tarwatsa zukatan wadanda suke kasuwancinsu da sunan koyarwa.
KASANCE TARE DA DIMOKURAƊIYYA TV A SHAFIN MU NA YOUTUBE 👇👇👇
“Muna cikin zamanin siyasa, wasu ‘yan siyasa na iya fara ba da dama, wato dai Suna iya cewa mun bujiro da wannan tsari ne don korar malamai.
“Kuna iya tunanin makaranta mai malamai 10 a tarihinmu amma idan kun ziyarci makarantar za ku ga uku kawai.
Amma kuma duk da hakan Sauran ba inda za a same su, amma suna karbar albashi,” inji shi.
A cewar Tambuwal, hakan yana kawo cikas ga aiwatar da ayyukan ci gaban malamai da dai sauransu.
Gwamnan wanda ya ke jawabi a wajen rabon kayan koyarwa da na karatu ga makarantun firamare a ranar Alhamis, ya bukaci shugaban hukumar ilimin bai daya na jihar da kada ya rubuta sunansa a makarantu.
Gwamnan ya yabawa hukumomin bada tallafi irinsu UNICEF da BESDA bisa tallafin da suke bayarwa wajen bunkasa ilimi a jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar Bello Gwiwa ya ce gwamnatin jihar ce ta siyo kayayyakin tare da karin tallafi daga UNICEF da BESDA.