Wadansu gamayyar Kungiyar matasan Arewa karkashin jagorancin Alhaji Nastura Ahmad Shariff ta yi kira ga dukkan jama’ar arewacin Nijeriya da su fito su yi zanga-zanga akan matsalar tsaro da ta addabi yankin a ranar Talata.
Za a yi wannan zanga zanga ne a dukkanin jihohi goma sha tara na arewacin Nijeriyar.
Zanga-zangar za ta kunshi kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya na farar hula, kana za a watsa ta a kafafen sada zumunta.