Jam’iyyar PDP ta gargaɗi Gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawalle daya guji haɗa baki da Majalisar Dokokin Jahar domin shirye-shiryen tsige Mataimakin sa Mohammed Gusau.
Babbar Jam’iyyar PDP tayi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaru na Jam’iyyar Debo Olugunagba ya sanyawa hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kashe mayakan ISWAP da dama a Tafkin Chadi — Inji Wani Rahoto
Jam’iyyar ta ƙalubalanci Gwamnan da ” kirkira da sanya faɗa a Jahar ta hanyar haɗa baki da Majalisar Dokokin Jahar domin fara yunƙurin tsige Mataimakin sa Mohammed Gusau wanda ya saba da doka, da Dimokuraɗiyya.
Jam’iyyar PDP ta kuma yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC data yi gaggawar kiran Matawalle daya tabbatar da cewa ba’a ci mutuncin Dimokuraɗiyya ba a Jahar Zamfara.
A cewar Jam’iyyar, a ɗorawa Matawalle alhaki idan aka samu karya doka wanda zai iya haifar da zubar da jinane a Jahar Zamfara, wanda kuma zai iya haddasa rikici a Najeriya, kamar yadda duniya ke gani.
“Duk wani yunƙuri na tsige Mataimakin Gwamna akan basu ƙarairaki zai haifar da faɗace-faɗace wanda zai iya haddasa karya doka da oda a Jahar.