Uba Sani ya mayar da Fom ɗin Takara, ya nuna godiya ga Soyayyar daya ke samu ga Al’umma
Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC Sanata Malam Uba sani ya nuna Jindaɗinsa game da yadda yake samun goyon bayan Al’ummar jihar Kaduna.
Sanatan ya bayyana Hakan a lokacin da yake mayarda da Form ɗin daya saya ya Kuma Cike na jam’iyar APC a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mamakon Ruwan Sama A Yobe: Gwamna Buni ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa
Sanatan ya ce “a yau na samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC na jihar Kaduna ta hanyar mayar da fom ɗin tsayawa takara dana nuna sha’awa zuwa ga hedikwatar babbar jam’iyyar mu na ƙasa dake Abuja.
Idan dai ba’a manta ba Sakataren Ƙungiyar (NOS) na Ƙasa, Mai Girma Sulaiman Mohammed Argungu ne ya karɓo fom ɗin a madadin Ɗan Takarar.
Manyan Jiga-Jigan jam’iyyar na jihar Kaduna, makusanta, abokai da magoya baya ne suka Sanatan zuwa hedikwatar jam’iyyar APC domin mika fom ɗin.
“Tabbas a tare za mu yi aiki domin ɗorawa da zurfafa abubuwan da suka dace wanda Shugaban mu kuma jagoranmu, Gwamna Nasir El-Rufai ya gadar mana”. Inji Sanatan
A halin Yanzu Sanata Uba sani shine Ɗan Takarar Gwamna Mafi samun karɓuwa a Jihar Kaduna.
Comments 1