Zan fara aiki ne daga awata ta farko a Ofis — Cewar Wani Ɗan Takara
Shugaban Kamfanin Jaridar Blueprint Kuma Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Niger a Jam’iyyar APC Alhaji Mohammed Malagi a ranar Talata yace zai fara aiki ne daga awa ta farko idan ya zama Gwamna domin ya cimma nasarar shi ta kawo gyara.
Malami ya kasance ɗaya daga cikin masu neman Takarar Gwamna a APC a Jahar Niger.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uba Sani ya mayar da Fom ɗin Takara, ya nuna godiya ga Soyayyar daya ke samu ga Al’umma
Yace zai ɗora daga inda wanda suka gabace shi suka yi wajen kawo ɗumbin ayyukan cigaba a Jahar.
Malagi ya bayyana haka a tattaunawar sa da Ƴan Jarida bayan ya mayar da Fom ɗin Takarar shi da Shuwagabannin Jam’iyyar a Abuja.
Yace Jahar Niger na ɗaya daga cikin Jahohin da Allah ya Albarkata wajen yawan Al’umma da Albarkatun Ƙasa, sai yasha alwashin yin Amfani da yawan jama’a wajen ciyar da Jahar a mataki na gaba, da zata yi gogayya da Jahohi a Najeriya.
Comments 1