Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jahar Enugu a ranar Talata ya rantsar da Mai Shari’a Ozoemena a matsayin sabon Jojin Jahar.
Ozoemena shine mutum na farko da aka naɗa a matsayin joji na rikon kwarya a Jahar na tsawon watanni 3 a lokutta mabanbanta , bayan ritayar tsohon Jojin, Mai Shari’a Priscilla Emehelu a ranar 7 ga watan Satumba na shekarar 2021.
Gwamnan ya bayyana cewar, matakin ƙaddamar da Mai Shari’a Ozoemena a matsayin muƙaddashin Jojin Jahar a ranar 7 ga watan Satumba na shekarar 2021, da sabunta naɗa shi a ranar 8 ga watan Disamba na shekarar 2021, bayan wa’adin sa ya ƙare, kamar yadda manyan joji suka bada shawara wanda ya tabbatar dashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hisbah ta ƙwace Kwalabanin Giya 1,906 a Jigawa
Dayake jawabi a lokacin rantsarwa a gidan Gwamnati, Ugwuanyi ya bayyana cewar bada muƙamin ya biyo bayan shawarwari da Hukumar kula da Ɓangaren Shari’a da kuma tabbatar da naɗin shi da Majalisar Dokoki tayi, a ƙarƙashin sashe 271 ƙaramin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.