Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin Duniya UNICEF ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Jami’ar Tarayya ta Kashere, da ke Jihar Gombe domin fara karatun digiri na biyu a fannin sadarwa don ci gaba da canza halayya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa, Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Misis Cristian Munduate, wadda ta jagoranci wata tawaga mai karfi daga hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, ta sanya hannu a madadin kungiyar kuma mataimakin shugaban jami’ar tarayya Kashere, Farfesa Umaru Pate, ya sanya hannu a babban dakin karatu.
Taron ya gudana ne a ranar Talata a harabar jami’ar .
KU KARANTA KUMA UNICEF Ta Horar Da Ma’aikatan Kiwon Lafiya Kan Hidima Ga Al’umma
Ms Munduate ta ce ziyarar da tawagar ta kai cibiyar ita ce don sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da jami’ar.
An tattaro cewa wannan shi ne irin wannan yarjejeniya ta farko a Najeriya da UNICEF da duk wata jami’a a kasar.
Da yake jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, Farfesa Umaru Pate ya ce hakan zai ba da damammaki na dorewar ci gaban karfin dan Adam a yankin arewa maso gabas da kuma fadin Najeriya.
Pate ya ce karatun digirin na biyu zai fara ne a zaman karatu na gaba saboda jami’ar za ta yi tsammanin neman masu bukatar karatun.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ce tare da yarjejeniyar fahimtar juna, UNICEF za ta tallafa wa kwas din na digiri na biyu da albarkatun dan Adam da kayan aiki don bunkasa ƙwararrun hanyoyin sadarwa na gaba waɗanda ke fahimtar abubuwan da suka dace na ci gaba musamman, batutuwan da suka shafi jin daɗin mata da yara.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Ya yabawa UNICEF saboda gano jami’ar da ta cancanci haɗin gwiwa da fahimtar juna.
A Wani Labarin Kuma Kotu Ta Kori Karar Da Ke Kalubalantar Nasarar Takarar Gwamna Yahaya
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da karar dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP Mohammed Barde ya shigar a gabanta kan gwamna Muhammadu Yahaya da hukumar zabe mai zaman kanta da wasu mutane biyu.
Sai dai kotun ta ki soke takarar gwamnan.