Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta cafke wani mutum mai suna Bamuwa Umaru, shekara 62 a duniya, bisa laifin bayar da cin hancin N1m domin a sako wani mai garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da cafke mutumin s wata sanarwa da ya rabawa ƴan jarida ranar Talata a birnin Kano. Jaridar Daily Nigerian ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Messi na shirin watsawa PSG ƙasa a ido, akwai yiwuwar ya koma Barcelona
“A ranar 16 ga watan Disamban 2022 da misalin ƙarfe biyu na rana, Bamuwa Umaru, mazaunin garin Shika cikin jihar Kaduna, ya tunkari jami’in da yake kula da tawagar daƙile garkuwa da mutane na ɓangaren bincike kan laifuka a rundunar ƴan sandan Kano, SP Aliyu Mohammed.
“Wanda yake zargin ya nemi da ya bayar cin hancin N1m domin a saki wani wanda ake zargi da garkuwa da mutane, Yusuf Ibrahim, mai shekara 27, mazaunin ƙauyen Danjibga a jihar Zamfara.” A cewar sa
Abdullahi Kiyawa yace wanda ake zargi da garkuwa da mutanen, tawagar dake atisayen dawo da zaman lafiya ƙarƙashin CSP Usman Abdullahi, DPO na Rijiyar Zaki, Kano, ne suka cafke shi.
“Wani direba da suka taɓa sacewa akan hanyar Funtua-Gusau sannan suka karɓi N500,000 kuɗin fansa shine ya gane Yusuf Ibrahim.”
Binciken farko da aka gudanar, Ibrahim ya amsa laifin sa inda ya ƙara da bayyana cewa yayi sace-sacen mutane da dama a garuruwan Sheme, Yankara, Faskari da Kucheri a cikin jihohin Katsina da Zamfara.
“Ibrahim ya kuma ƙara bayyana cewa tawagar su ta halaka aƙalla mutum 10 da suka yi garkuwa da su, inda shi kaɗai kawai ya halaka mutum biyu.”
“Waɗanda ake zargin za a tura su kotu da zarar an kammala bincike.” A cewar sa.
Kotu Ta Kori Karar Da Ke Kalubalantar Nasarar Takarar Gwamna Yahaya
A wani labarin na daban kuma kotu tayi watsi da ƙarar da aka shigar kan gwamnan jihar Gombe.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da karar dan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP Mohammed Barde ya shigar a gabanta kan gwamna Muhammadu Yahaya da hukumar zabe mai zaman kanta da wasu mutane biyu.
Sai dai kotun ta ki soke takarar gwamnan.