Sanata Oluremi Tinubu, uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed, za ta jagoranci tawagar shugabannin mata a yammacin ranar Alhamis domin ganawa da kwamitin aiki na jam’iyyar a Abuja.
Wannan ci gaban na zuwa ne sa’o’i 24 bayan maigidanta ya jagoranci abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima da wasu jiga-jigan jam’iyyar zuwa sakatariyar a ranar Laraba data gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: PDP Ta Nada Wabara A Matsayin Sabon Shugaban BoT Na Jam’iyyar
Za a yi muhawarar siyasa da misalin karfe 4:00 na yamma.
Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulki, Oluremi ana sa ran za ta tattauna da shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Mrs Betty Edu, kan tattaunawa da ke damun su kan shigarsu tukura gabanin yakin neman zabe na ranar 28 ga watan Satumba da zabukan 2023.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an karfafa bayanan tsaro a sakatariyar jam’iyyar ta kasa gabanin ziyarar da tawagar Sanatan ta kai.
Kamar dai yadda aka shaida a ranar Laraba, za a nemi hanyar tantancewa tare da gudanar da bincike kan maziyartan da ke shigowa harabar sakatariyar domin kula da zirga-zirgar mutane da ababen hawa domin tsaro.
A wani labarin kuma, Za Mu Binciki Musabbabin Mutuwar Yara A Kasar Mu—- Gwamnatin Gambiya
Darektan ma’aikatar lafiya ta yammacin Afirka Mustapha Bittaye ne ya bayyan cewa, Gwamnatin Gambia na binciken ko mutuwar kananan yara sakamakon ciwon koda a yan watannin nan, na da nasaba da wani maganin Zazzabi da ake hadashi a kasar. .
Bincike ya nuna cewa an gano wannan matsalar na koda a tsakanin yara a kasar da ke da shekaru biyar a ƙarshen Yuli wannan shekara.