Wata tsohuwa mai suna Halimatu Atta mai shekaru 90 da aka sace daga jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a watan Maris ta samu ‘yanci.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An sake ta ne tare da diyarta da wasu mutane biyu da aka sace, a cewar mawallafin da ke zaune a Kaduna, Tukur Mamu, wanda ya yi shawarwarin a sako wasu daga cikin wadanda abin ya shafa.
Wani Kwamishina Ya Shaki Iskar Yanci, Bayan Yan Garkuwa Sun Kwamushe Shi
“Zan iya tabbatar da cewa a safiyar ranar Juma’ar nan, masu garkuwa sun sako wasu mutane hudu da harin jirgin kasa ya shafa.”
“Daga cikin wadanda aka saki a ranar Juma’ar akwai tsohuwar da aka sace, kaka, Mama Halimatu Atta tana da shekaru 90 a duniya. Har ila yau, an sake sakin diyarta mai shekaru 53, matar aure, da kuma Adama Atta Aliyu, (matar da ta nuna jarumtaka a faifan bidiyo na baya tana nuna rashin amincewa da kalubalantar wadanda suka yi garkuwa da ita tare da nuna rashin amincewarsu da rashin sakin su).
“Mutane hudun da aka sako sun bar ofishina. Sun ce sun zo ne baki daya domin su gode min kan kokarin da na yi a baya na yin sulhu a madadinsu da kuma shawo kan wadanda suka sace su da su yi watsi da barazanar aiwatar da su tare da rokon duk masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya da ta kara kaimi a matsayin sharadin da ya rage. Mutane 23 da suka rage a dajin abin tausayi ne,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Sauran biyun da lamarin ya ritsa da su; su ne Mohammed Sani Abdulmaji (M.S Ustaz) da Alhaji Modin Modi Bodinga.