Wadanda suka yi garkuwa da wani jami’in DSS a yankin Abaji da ke Abuja suna neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, kafin su sako shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin jami’an DSS inda suka yi awon gaba da daya daga cikinsu, amma kakakin hukumar ya musanta wannan rahoton.
Wata majiya mai tushe wacce ta bayyana wa wakilin Jaridar Daily Trusta a ranar Lahadin da ta gabata, ta ce an samu tuntubar wadanda suka yi garkuwa da jami’in, kwana biyu bayan sace shi.
“Su (DSS) suna ci gaba da tattaunawa da su duk da cewa (masu garkuwa da jami’in) sun dage kan neman kudin fansan Naira miliyan 20,” inji shi.