Sanata Smart Adeyemi ya caccaki Babban Bankin Najeriya, CBN, Gwamna Godwin Emefiele, inda ya ce an sake fasalin kudin Naira ne domin a wahalar da ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, ya bayyana manufar rashin kudi a matsayin rashin zuciya, duba da irin wahalhalun da ake fuskanta ba tare da an kawo karshe ba.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Okey Ahiwe Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamna Na PDP
Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar, Adeyemi ya yi zargin cewa gwamnan babban bankin na yin aikin da wasu ‘yan fadar shugaban kasa ne don ganin jam’iyyar APC ta fadi zabe a karshen watan nan.
A cewarsa, manufar ita ce tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta ci zabe ba ganin cewa tsarin tsabar kudi yana haifar da damar zaben APC yayin da ‘yan kasar ke kukan rashin kudi don biyan bukatunsu na yau da kullum.
Adeyemi ya ce a halin yanzu talakawa da ke cikin wahala suna zagin gwamnan babban bankin kasar yayin da ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa baki.
“Ina goyon bayan bukatar canza kudin, amma ba na goyon bayan hanya da kuma yadda ake gudanar da dukkan ayyukan.”
“Da yawa sun mutu saboda ba su da kuɗin siyan magunguna, wasu kuma sun mutu saboda hawan jini, yayin da manyan mutane suna da tsabar kudi a gidajensu.”
Kwanaki bakwai da Shugaba Buhari ya bukaci a bashi yayi tsayi da yawa don kawo sauyi,” inji shi.
Sanatan ya dage cewa wahala ta zama ba za ta iya jurewa ba a yanzu kafin lokaci ya kure, kamar yadda ya ce, a matsayinsa na zababben Sanata, mutane sun rika tambaya, ta yaya za su biya kudi su samu kudi?
A wani labarin kuma: Aikin Gwajin Amfani Da Na’urar BVAS: INEC Ta Zabi Kananan Hukumomi 6 A Kano
Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kebe kananan hukumomi biyu kowacce daga gundumomin sanatoci uku na jihar Kano domin gudanar da aikin gwajin tantance.masu zabe ta hanyar amfani da na’urar BVAS.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta nuna cewa za a kammala atisayen da za a fara da karfe 9:00 na safe da karfe 2-00 na rana a yau Asabar.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa an zabi kananan hukumomin Gwale da Kumbotso a Kano ta Tsakiya, Bichi da Dawakin Tofa a Kano ta Arewa yayin da Wudil da Rano aka zaba a Kano ta Kudu.