Mayakan Taliban biyu da wani farar hula sun rasa rayukansu a safiyar yau Laraba, sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kai kan wani shingen binciken ababen hawa a gabashin Afghanistan, in ji hukumomin tsaro da shaidun gani da ido.
Harin da aka kai a birnin Jalalabad shi ne na baya -bayan nan da aka kai wa yan kungiyar Taliban a lardin Nangarhar, wanda tsawon shekaru shi ne babban sansanin yan kungiyar IS reshen Afghanistan.
Wata majiyar tsaro da shaidun gani da Ido sun ce, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kai hari kan shingen binciken ababen hawa a gundumar Ghawchak da ke Jalalabad, inda suka kashe masu gadin Taliban biyu, da wani farar hula da ke tsaye a kusa da shingen.
Wani jami’in Taliban ya tabbatar da harin, amma yace, wadanda suka mutu dukkansu fararen hula ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC ta kama Mutane 30 da zargin damfara ta yanar Gizo
A wani lamarin kuma, mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mayakan Taliban guda biyu sun jikkata yayin da suke kokarin kwance wani abu mai fashewa a Jalalabad.
Sai dai har kawo hada wannan rahoto, ba’asami wani cikakken Karin bayani kan wannan harin ba.
A wani labarin Kuma na daban.
‘Yan sanda a Kano sun cafke wata mata mazaunin unguwar Rijiyar Zaki Quarters dake aika wa‘ yan kasuwa gargadin karban bashi na bankin bayan sun sayar da kayansu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata a Kano, yace“A ranar 12 ga Satumba, da misalin karfe 6:30 na yamma, yan kasuwa uku, Jamilu Musa, Aliyu Inusa da Sadiya Muhammad, wadan suke mazauna jihar Kano a wurare daban daban sun shigar da rahoton cewa tsakanin ranar 11 ga Satumba zuwa 14 ga Satumba, wanda ake zargin ta sayi kayan kundi na Naira 57, 000 daga shagunan su.
“Wadanda abin ya rutsa da su sun shaida wa‘ yan sanda cewa wanda ake zargin ta kirkiri tare da kuma aika da sakonnin karya, zuwa gare su amma ba su fahimci cewa faifan lamunin na bogi ne ba sai bayan da ta bar shagunan su, ”in ji kakakin‘ yan sandan.
Haruna Kiyawa ya ce, lokacin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya samu rahotannin, ya umurci tawagar jami’an binciken da SP Daniel Amah dake jagoranta da su gano tare da cafke wanda ake zargin da aiki kuma ya sami nasarar cafke wanda ake zargi yayin da take ƙoƙarin tattara kayan daga wasu shagunan ta amfani da wannan hanyar.
“A lokacin bincike na farko, wanda ake zargin ta amsa laifin ta, inda ta ce ta kware wajen kirkirar bayanan karya da karya don damfarar wadanda abin ya shafa,” in ji Haruna-Kiyawa.Ya kuma bayyana cewa an shigar da wasu korafe korafe guda hudu bayan da aka kama wanda ake zargi inda ya kara da cewa za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.