Ana zargin wasu mutane dauke da makamai a ranar Alhamis sun bindige wani lauya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
An kashe lauyan, Barista Benedict Azza ne lokacin da ‘yan bindigar suka yi yunkurin sace shi a gidansa da ke unguwar Saminaka, bye-pass a Gusau.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Majiyoyi sun ce lauyan ya yi yunkurin tserewa ne ta hanyar garzaya da motarsa tare da shiga babban titin, sai dai maharan sun bi shi inda suka harbe shi har sau uku.
Mahaifiyar Dan Majalissar Wakilai Ta Rasu Tana Da Shekaru 111 Aduniya
Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA a jihar Zamfara ta tabbatar da kisan lauyan a wata sanarwa da shugaban kungiyar Barista Junaidu Abubakar ya fitar ranar Juma’ar nan.
A cewar Mista Abubakar, gawar marigayi a lokacin ta kasance an bar ta a bakin titi hanyar wucewa kusa da ofishin FRSC.
“A jiya da misalin karfe 22:30 na dare, ina gidana, na samu kiran waya daban-daban guda uku daga abokan aikinmu suna sanar da ni cewa B.T. Azza Esq. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe shi, kuma gawarsa na kwance a bakin hanya a kan hanyar Bye-pass kusa da ofishin FRSC, da ke Gusau.”
“Yan bindiga 2 da ba a san ko su wanene ba wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka zo kan babur ne suka harbe BT Azza har lahira. Bayanai sun nuna cewa, ‘yan bindigar sun so yin garkuwa da shi ne a gidansa da ke Unguwar Saminaka, a bayan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC), shedkwatar Byepass, da ke Gusau, amma ya samu nasarar tserewa, ya tuka motarsa da gudu zuwa bakin titi, inda ‘Yan bindigar suka bi shi suka harbe shi har lahira.”
A ci gaba da tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawunta, SP Mohammed Shehu, ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa an fara gudanar da bincike domin gano al’amarin da ya yi sanadin mutuwar Barista.
Shehu ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da abin ya shafa suna tsara dabarun gina kwarin gwiwar mazauna babban birnin da kuma inganta harkokin tsaro a fadin jihar.